Turkiyya za ta cigaba da zama na musanman da Girka akan Bahar Rum

Turkiyya za ta cigaba da zama na musanman da Girka akan Bahar Rum

Tawagar rundunar sojojin Turkiyya da na Girka za su cigaba da tattaunawa na musanman karkashin inuwar NATO a mako mai zuwa.

Tawagar sojojin Turkiyya da Girka sun fara zaman ne na mausanman mai take "hanyar warwarewa" bayan tattaunawar da shuagaban kasar Tiurkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi da babban sakatare janar na NATO Jens Stoltenberg.

Sakamakon tarurrukan da aka gudanar a Hedikwatar NATO, a ranar 2 ga watan Oktoban shekarar 2020 an sanar da cewa an samu fahimtar juna akan "ka'idojin gama gari".

Dangane ga bayanan da aka samo daga ma'aikatun tsaron kasar Turkiyya, kasancewar rashin damar halartar taron da Girka ba ta yi ya sanya ba'a gudanar da taron ba na dan wani lokaci. A halin yanzu dai ana shirin sake fara zaman a mako mai zuwa, ana dai tattaunawa ne akan lamurkan warware lamurkan Bahar Rum.

 


News Source:   ()