Shugaban masana'antun tsaron kasar Turkiyya, Isma'il Demir, ya bayyana cewa, nan gaba kadan za a kaddamar da wani kamfanin tauraron dan adam wanda ke hada karfi da karfe a
nazarin fasahar tauraron dan adam.
Demir ya yi sharhi game da Ayyukan Harkokin Sararin Samaniyan Turkiyya a cikin jawabinsa a Jami'ar Istanbul.
Tare da jaddada cewa ba da dadewa ba Turkiyya za ta sanya hannu kan wani muhimmin shiri na tauraron dan adam, inda ya kara da cewa,
"Za'a samar da katafaren kamfanin tauraron dan adam ta hanyar hadakar kwararrun kamfanoni masu iyawa daban-daban."
Turkiyya na da niyyar aika na'ura zuwa wata a shekarar 2023 inda kuma take shirin aika bil adama cikin wata a shekarar 2028.
Wani muhimmin mataki a cikin shirin shi ne a tura dan sama jannati Baturke na farko zuwa sararin samaniya a matsayin wani bangare na aikin kimiya.
An shirya cewa za a fara tantance 'yan jannatin da za'a tura zuwa duniyar watan nan ba da jimawa ba