Turkiyya tare da hadin gwiwar Mekziko ta kai kayan agaji na ton 10 ga kasar Haiti

Turkiyya tare da hadin gwiwar Mekziko ta kai kayan agaji na ton 10 ga kasar Haiti

Kasar Turkiyya tare da hadin gwiwar kasar Mekziko ta kai gudunmowar kayayyaki ga kasar Haiti sabili da matsal;olin da al'umman wasu yankin kasar suka shiga bayan afkuwar girgizar kasa.

Hukumar Hadin Kan Turkiyya (TIKA) ta aike da kayan abinci da na tsafta zuwa Haiti, inda ake samun karuwar mace -mace, raunuka bayan girgizar kasa mai karfin maki 7.2.

Jakunkunan da TIKA ta bayar an kai su Haiti ne ta jiragen sama na soji da na jirgin ruwan Mexico.

Kungiyoyin Kare Hakkokin Jama'a na Gwamnatin Haiti sun karbi kayan agajin da aka kawo don rarraba kayan zuwa yankunan da girgizar kasa ta fi shafa.


News Source:   ()