Kasar Turkiyya ta yiwa kasar Najeriya ta'aziyyar rasuwar shugaban hafsan Sojojin Kasa Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da wasu 11 sanadiyar hatsarin jirgin sama.
Kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya ta sanar,
"Muna bakin cikin samun labari cikin alhini na faduwar jirgin sama mallakar sojojin saman Najeriya sabili da rashin kyawon yanayi lamarin da ya yi sanadiyar rasa rayuwar kwamandan sojojin kasar kasan laftanar Janar Ibrahim Attahiru da wasu 11"
Sanarwar ta kara da cewa, muna masu taya kasar Najeriya bakin cikin afkuwar wannan lamarin, muna adduar samaun rahamar Allah ga wadanda suka rasa rayukansu da kuma mika sakon ta'ziyya ga 'yan uwansu da alumman kasar baki daya"