Turkiyya ta yiwa Iraki ta'aziyya akan rasa rayuka a gobarar asibitin da ake jinyar masu Korona

Turkiyya ta yiwa Iraki ta'aziyya akan rasa rayuka a gobarar asibitin da ake jinyar masu Korona

Turkiyya ta mika sakon ta'aziyya akan rasa rayukan da aka yi sakamakon fashewar wani abu a Asibitin Hatip da ake kula da marasa lafiyar da suka kamau da Korona a Baghdad babban birnin Iraki.

Kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta sanar a rubuce, muna masu bakin cikin samun labarin afkuwar fashewar wani abu da ya haifar da kamawar  wuta a asibitin da ake jinyar masu fama da Covid-19, lamarin da ya yi sanadiyar rasa rayukan marasa lafiya da masu jinyarsu da dama a Baghdad.

Sanarwar ta kara da cewa,

"Muna masu mika sakon ta'ziyya ga yan uwan wadanda suka rasa rayukansu da kuma ga kasar Iraki baki daya, muna masu fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata"


News Source:   ()