Turkiyya ta yiwa Amurka ta'aziyya

Turkiyya ta yiwa Amurka ta'aziyya

Turkiyya ta mika ta'aziyya da kuma jajantawa Amurka  kan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon rushewar wani gini a jihar Florida.

A cikin wata rubutacciyar sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar, an bayyana bakin cikin samu labarin cewa akwai wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata a ibtila'in, kuma mutane da yawa sun kasance a karkashin baraguzan ginin sakamakon rushewar wani bene mai hawa 12 a ranar 24 ga watan Yuni a Miami Dade, Florida.

A cikin sanarwar an kara da cewa,

"Muna nuna alhininmu ga mutane da gwamnatin Amurka da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka ji rauni." 

An sanar da cewa mutane 4 sun rasa rayukansu sakamakon rushewar wani bangare na bene mai hawa 12 a ranar 24 ga watan Yuni a Miami Dade, Florida, Amurka, kuma ba a ji duriyar mutane 159 da ake tunanin suna karkashin baraguzan ginin.


News Source:   ()