Turkiyya ta yi tir da Allah wadai akan aika-aikan kone Alkur'ani mai tsarki don nema tada zaune tsaye da tsokana a kasar Sweden.
Kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta sanasr a rubuce,
"Muna masu makutar yin tir da Allah wadai akan mummuna aikin tsokana da wani makiyin addinin Islama da magoya bayansa wanda yazo daga Denmark zuwa garin Malmo a Sweden ya yi da Alkur'ani mai tsarki"
Sanarawar ta kara da cewa, wannan aika-aikan neman tada zaune tsaye ya sabawa ka'ida da al'adar Tarayyar Turai.
Sanarwar ta kara da cewa wannan mummunan aika-aikan da aka yiwa Alkur'ani mai tsarki na nuna irin kalubale da barazanar da 'yan uwanmu Musulmi ke fuskanta a Turai.
Sanarawar ta kara da cewa matakin da hukumomin Sweden suka dauka na kame wadanda suka aikata wannan aika aikan ya dace, kuma muna kira ga kasar da ta ci gaba da daukar irin wannan matakin akan duk ire-iren wadanan aika-aikan tsokanan al'umman Musulmi.