Kasar Turkiyya ta yi tir da Allah wadai akan harin da aka kai da wuka a Ingila lamarin da ya yi sanadiyar rayukan mutane uku.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya ta fitar da sanarwa a rubuce inda ta bayyana cewa,
"Wannan harin zubar da jini, hari ne na ta'addanci wanda 'yan ta'adda suka sake nuna barnarsu. Muna masu mika sakon ta'aziyya ga kawarmu da muke musayar bayanai da ita a koda yaushe. Muna masu fatan samn hankuri ga wadanda ga 'yan uwan wadanda suka rasa rayukansu da kuma samun saukin wadanda suka raunana cikin sauki"
A marecen jiya ne aka kai hari da wuka a garin Reading mai nisan kilomita 60 daga babban birnin Birtaniya watau Landan a inda aka raunana mutum uku da kuma kashe wasu uku da wuka.