Turkiyya ta yi murnar cire Sudan daga cikin sunayen kasashe masu taimakawa ta’addanci

Turkiyya ta yi murnar cire Sudan daga cikin sunayen kasashe masu taimakawa ta’addanci

Kasar Turkiyya ta yi maraba da hukuncin Amurka na cire Sudan daga cikin jerin sunayen kasashen dake taimakawa ta’addanci matakin da aka dauka bayan shekaru 27.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar  Turkiyya Hami Aksoy ya bayyana cewa “muna kallon matakin Amurka na cire Sudan daga cikin kasashen dake taimakawa ta’addanci a matsayin matakin da ya dace”

Aksoy ya kara da cewa Turkiyya ta jima tana kira da a yi haka inda kuma ta kasance kasar dake kalubalantar takunkumin gefe guda.

Ya kara da cewa "Kasarmu za ta ci gaba da taimakawa kafa  demokaradiyya da gudanar da sauye sauye masu inganci a kasar Sudan.”


News Source:   ()