Turkiyya ta ba da rahoton cewa tana bin lamurkan cikin gida da ke afkuwa a Amurka bayan zaɓen shugaban ƙasa da matukar damuwa.
A cikin sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar, an bayyana cewar ana bin abubuwan da ke faruwa a cikin Amurka, da suka hada da ƙoƙarin mamaye ginin Majalisa da masu zanga-zangar suka yi jiya da matukar damuwa.
Sanarwar ta kara da cewa "Muna gayyatar dukkan bangarorin da ke Amurka da su yi kokarin daidaitawa kuma su yi aiki mai ma’ana. Mun yi imanin cewa Amurka za ta shawo kan wannan rikicin cikin gida na siyasa yadda ya kamata.”
A cikin sanarwar, an ba wa ‘yan asalin Turkawa da ke Amurka shawarar kaurace wa wurare masu cunkoson mutane da wuraren da ake gudanar da zanga-zanga.