Turkiyya ta yi tir da Allah wadai a kan kisan shugaban Haiti, Jovenel Moise.
A cikin wata rubutacciyar sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar, an bayyana cewa suna bakin cikin samun labarin cewa Shugaban Haiti ya rasa ransa sakamakon mummunan harin da aka kai gidansa.
Sanarwar ta kara da cewa, "Muna tir da Allah wadai da wannan mummunan harin kuma muna fatan za a gurfanar da wadanda suka aikata kisan a gaban shari'a cikin gaggawa." Turkiyya ta kuma mika sakon ta'aziya ga iyalin Moise da mutanen Haiti masu abokantaka da Turkiyya.
An kashe Shugaba Moise mai shekaru 53 a duniya a wani hari da wata kungiya mai dauke da makamai ta kai gidansa.
Matarsa, Martine Moise wacce ta ji raunuka a harin tana cikin mawuyacin hali.