Turkiyya ta taya Antonio Guterres murna akan sake nadashi a matsayin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) a karo na biyu.
A cikin rubutacciyar sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen ta fitar, an bayyana cewa, Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shawararta kan sake nada Guterres kan wannan mukamin na wa'adin shekaru 5 na biyu a ranar 18 ga watan Yuni 2021.
A cikin sanarwar an bayyana cewa,
"Muna taya Mista Guterres murnar sake nada shi a matsayin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya. Muna da cikakken yakinin cewa alakar kut-da-kut da kawancen da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Guterres ya kulla da kasarmu a lokacin mulkinsa na yanzu zai ci gaba a lokutta na gaba."
An jaddada cewa, Turkiyya za ta ci gaba da karfafa gudummawar da take bayarwa ga aikin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya daidai da manufar cimma manufa da kuma ka'idojin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniyan.
Babban abin alfahari ne ga kasarmu cewa bayan sake nada Antonio Guterres an kuma zabi dan kasarmu Volkan Bozkir wanda ya rike mukamin shugaban zauren majalisar karo na 75 a matsayin daya daga cikin kwamitin zartarwa.