Turkiyya ta taimakawa Sudan ta Kudu da kayayyakin abinci

Turkiyya ta taimakawa Sudan ta Kudu da kayayyakin abinci

Gwamnatin Turkiyya ta taimakawa kasar Sudan ta Kudu da abinci sabili da matsalar karancin abinci da kasar ke fama dashi.

An sanar da cewa za’a rabawa sojojin dake filin horaswa kayayyakin abincin ne musanmamn a yankunan da ake fuskantar karanci abinci a kasar.

Mai bayar da shawara akan harkokin tsaro a kasar Sudan ta Kudu Tut Gatluak, ya yiwa gwamnatin Turkiyya godiya a yayinda ya ke karbar abincin a matsayin gwamnatin kasarsa.

A yayinda ambasadan Turkiyya a kasar Sudan ta Kudu  Erdem Mutaf ke mika kayayyakin abincin  ya jaddada goyon bayan da Turkiyya ke baiwa kasar Sudan ta Kudu domin samun lumana da sukuni.

Ya kara da cewa “Taimakon kayan abincin da ya kain a ton 11 da nike mikawa jami’i  Tut Gatluak  a ya una daga cikin alamun Turkiyya na taimakawa harkokin yau da kullun na kasar Sudan ta Kudu”

A yayinda da yake kuma ziyarar ma’aiakatun kasar dake Juba babban birnin Sudan ta Kudu ya nanata cewa Turkiyya na shirin kara inganta hulda tsakaninta da Sudan ta Kudun.

 


News Source:   ()