Turkiyya ta taimakawa kasar Somaliya da motocin Landiroba har guda 12 wadanda anka mikawa rundunar sojin kasar domin taimakawa tsaron kasar.
Ma'aikatar tsaron kasar Turkiyya (MSB) ce ta fitar da sanarwar da cewa,
"An mikawa sojojin kasar Somaliya motocin Landiroba 12 a tasar jirgin ruwan dake babban birnin kasar Mogadishu. Muna yiwa 'yar uwarmu Somaliya murnar samun wadannan motocin da kuma fatan alkhairi"