Kasar Turkiyya ta taimakawa Pakistan da kayayyakin kimiyya da kayan aiki na zamani domin yaki da farin dango.
Hukumar Hadin Kai da Taimako ta Turkiyya wato TIKA ta mikawa Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasar Pakistan NDMA na’urori masu fesa magani da kuma ruwan maganin kashe kwari.
Bikin mikawa da kayan aikin ya samu halartar ministan harkokin abinci Fakhar Imam na kasar Pakistan da kuma jakadan Turkiyya a Pakistan Mustafa Yurdakul da kuma shugaban TIKA a babban birnin Pakistan Islamabad Gokhan Umut.
A taron Imam ya godewa gwamnatin Turkiyya akan namijin kokarin da ta yi da kuma diyaucin da ta nuna.
Inda ya kara da cewa “gwamnati na kokarin daukar matakai domin inganta noma a kasar sabili da haka gudunmowar kayan aikin da Turkiyya ta bayar zasu taimaka wajen inganta noma a kasar”