Ma'aikatar addinin kasar Turkiyya ta aike da kayayyakin taimako zuwa ga iyalai 400 da annobar ambaliyar ruwa ta shafa a yankin Umdurman da Kalakle dake karkashin babban birnin Sudan Hartum.
Tun daga watan Yuni kawo yanzu dai ake fama da tsananin ruwan sama da ya haifar da cikowar rafin Nilu wanda ya yi sanadiyar kwararar ruwa da ya yi sanadiyar rushewar gidaje wanda ya taba dubban iyalai.
Hukumar ta rabawa iyalai 250 a yankin Kalakle dake kusa da rafin Nilu, iyalai 150 a yankin Umdurman kayayyakin abinci da suka hada da sukari, garin fulawa, man abinci, kayan lambu da makamantansu da kuma barguna da sauran kayan magance sanyi.