Turkiyya ta soki shugaban Austria akan goyon bayan Isra’ila

Turkiyya ta soki shugaban Austria akan goyon bayan Isra’ila

Mai magana da yawun shugaban kasar Turkiyya a ranar Juma’ar da ta gabata ya soki shugabar gwamnatin Austria Sebastian Kurz kan yadda ya daga tutar Isra’ila a kan rufin ginin gidan gwamnati a Vienna a yayin hare-haren da gwamnatin yahudawan ta kai wa Falasdinu.

"Wannan shi ne abin da ke karfafa Isra'ila don ci gaba da kai hare-hare kan mutanen Falasdinu," in ji Ibrahim Kalin a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Tweeter. "Ina fatan wadancan 'yan Austriyan da Turawan da ke da hankali da dabi'a za su yi watsi da irin wannan siyasar ta ban kunya."

Kurz ya wallafa a shafinsa na Tweita wani hoto dauke da rubutu wanda ke cewa: "A yau an daga tutar Isra'ila a saman gidan gwamnatin tarayya a matsayin wata alama ta hadin kai tare da #Isra'ila ... Muna tare da Isra'ila."


News Source:   ()