Kasar Turkiyya ta soki shirin gudanar da zaben da gwamnatin Bashar al-Assad ke shirin yi a yayinda kasar ke cikin halin kakanikayi.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya Tanju Bilgic ya bayyana cewa "Sanarwar da gwamnatin Siriya ta yi na gudanar da zabe a ranar 26 ga watan Mayu, 2021 ya sabawa kaidojin da Majalisar Tsaron Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2254”
Bilgic ya bayyana cewa zaben ba zai kasance sahihi ba sabili da halin da kasar ke ciki kuma miliyoyin al’umman kasar dake neman mafaka a kasashen waje ba zasu samu damar kada kuri’a ba, wannan zabe ne da kungiyoyi da hukumomin kasa da ksa ba zasu amince dashi ba.
Ya kara da cewa Turkiyya za ta ci gaba da taimakwa bisa tsarin Majalisar Tsaron Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2254 domin samar da lumana a kasar Siriya cikin ruwan sanyi.