Sojojin ruwan kasar Turkiyya sun daura damarar mayar da jirgin ruwan TCG Andolu a matsayin wanda zai fara dakon jirage marasa matuka na farko a doron kasa.
A 'yan kwanakin nan kanfanin jirage marasa matukan kasar Turkiyya da ta yi tasiri a kafafen yada labaran Amurka akan ci gaba da ta samu ta dauara aniyar samar da jirgin ruwa wanda jirage marasa matuka zasu fara iya tashi da sauka a kansa.
Kamar yadda jaridar Forbes ta sanar shugaban kanfanin Baykar wanda ke samar da jirage marasa matuka a kasar Turkiyya Haluk Bayraktar ya bayyana cewa za'a mayar da jirgin ruwan TCG Anadolu a matsayin wanda zai iya dakon jirage marasa matuka.
Kamar yadda kanun labarin na Forbes ya bayyana " Wannan shi ne jirgin ruwan da Turkiyya ta samar wanda zai fara iya daukar jirage masara matuka da kuma wanda zasu iya tashi da sauka akansa na farko a dorona kasa"