Turkiyya ta sake aikewa da kayayyakin taimako Lebanon

Turkiyya ta sake aikewa da kayayyakin taimako Lebanon

An sanar da cewa jirgin sojan kasar Turkiyya kirar A 400M ya sauka da kayayyakin taimako na kiwon lafiya a Beirut babban birnin kasar Lebanon.

A kwanakin baya ma jirgin sojojin Turkiyya kirar A400 ya kai kayayyakin taimako bayan fashewar da aka samu a wani tashar jirgin ruwa dake kasar.

Kungiyoyi da dama na kasar Turkiyya sun kai dauki inda suka gudanar da ayyukan ceto da tallafawa al'umma da suka kasance cikin mawuyacin hali bayan mummunan fashewar abu a Beirut.

Haka kuma Hukumar TIKA ta kasar Turkiyya zata aika da tan 400 na alkama domin rabawa wadanda suka shiga halin kakanikayi a birnin.

 


News Source:   ()