A ci gaba da yakin da ake yi da sabon nau'in kwayar cutar Coronavirus (Kovid-19), Turkiyya ta mika wasu allurai dubu 26 na kanfanin Sinovac zuwa Jamhuriyar Cyprus bangaren Turkiyya.
Alurar rigakafin da aka kai ta jirgin daukar marasa lafiya na Ma'aikatar Lafiya ta Turkiyya an mika su ga jami'an Ma'aikatar Lafiyar Cyprus a Filin jirgin saman Ercan.
Adadin allurar rigakafin da Turkiyya ta aika zuwa Cyprus ya kai allurai 216,000. An shirya cewa za a aika allurai 300,000 na rigakafin zuwa Cyprus a karshen Yuli.
Ministan Lafiyar Cyprus Unal Ustel, a bayaninsa ga gidan Radiyo da Talabijin Bayrak (BRT) dangane da tattaunawar da ya yi da takwaransa na Turkiyya, ya jaddada cewa za a tura wasu adadin alurar rigakafi daga Turkiyya zuwa Cyprus kowane mako har zuwa karshen watan Yuli.