Gidauniyar Kula da Al’amuran Addinai ta Turkiyya (TDV), domin wata mai alfarma na Ramadan ta aike da “Kyakkyawan Abincin” ga kasashen Nijar, Bosniya da Herzegovina.
Jami'in gidauniyar TDV Yahya Uyar, a cikin rubutaccen bayanin nasa, ya ce an isar da taimako daga Turkiyya ga mabukata a Nijar.
Uyar ya ce sun ba da taimakon abinci ga iyalai 1500 a Yamai babban birnin kasar da sauran yankuna, sannan kuma sun bude rijiyoyin ruwa da mabubbugan ruwa a sassan kasar daban-daban.
A halin yanzu, Ofishin Jakadancin Turkiyya da ke Sarajevo da hadin gwiwar Ofishin Ayyukan Addini, ta rarraba wa mabukata kayan taimako a Busovaca dake tsakiyar Bosnia da Herzegovina.
An bayyana cewa an rarraba "Kyakkyawan Abincin" a biranen Olovo, Fojnica, Mostar, Kakanj, Srebrenica da Kiseljak da ke Bosniya da Herzegovina, kuma za a isar da kusan fakiti 400 ga adiresoshin har zuwa karshen Ramadan