Turkiyya ta mayar wa Amurka da martani akan rahoton fataucin mutane

Turkiyya ta mayar wa Amurka da martani akan rahoton fataucin mutane

Turkiyya ta bayyana rahoton fataucin bil adama da Amurka ta fitar a matsayin wani "misali na munafunci"

A cikin rubutacciyar sanarwa daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya, an bayyana cewa a cikin rahoton Fataucin Bil Adama na 2021 na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, an tabbatar da cewa Turkiyya ta kara yaki da fataucin mutane,

"Duk da wannan, akwai zarge-zargen marasa kan gado da suka kunshi kungiyoyi masu zaman kansu, lamarin da ke kokarin safawa kokarin da Turkiyya ke yi kashin kaji."
A cikin sanarwar, Turkiyya ta yi iya kokarinta don hana aikata laifukan fataucin mutane, hukunta wadanda suka aikata ta da kuma kare wadanda ake zalunta, da kuma yaki mai tasiri kan fataucin mutane, wanda aka shirya tare da taken "Mutum mai 'yanci, al'umma mai karfi, Turkiyya mai dimokiradiyya" wanda ya samu sanya hanun Shugaba Recep Tayyip Erdogan

"Mun yi watsi da korafe-korafen da ke nuna baiwa yara makamai ." A cikin sanarwar, an kara jaddada cewa Turkiyya na daga cikin hukumomin kasa da kasa kan kare hakkin yara, ciki har da wadanda Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta amince da su, kuma "tarihin nata ba shi da tabo".

A cikin sanarwar, an ja hankali da cewa irin wannan zargin na Amurka, wacce ke nuna goyon baya ga kungiyar ta'adda ta 'yan aware ta PKK-PYD-YPG, gami da taimakon makamai, da ke daukar yara kanana a ayyukan ta'addanci a Siriya da Iraki, shi ne mafi ban mamaki misali mai fuska biyu kuma na munafunci.

Kungiyar da ake kira "Syrian Democratic Forces" karkashin jagorancin kungiyar ta'adda ta 'yan ta'addar aware PKK / YPG ta aikata laifuka da yawa da manyan laifuka irin su tilasta daukar yara kanana, sata, hana' yanci, amfani da makarantu don dalilan soja, an bayyana hakan a rahoton Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na Musamman kan Yara da Rikicin Virginia wato Gamba wanda aka fitar a ranar 21 ga watan Yunin shekarar 2021, duk da haka rashin ambatar kungiyar a cikin rahoton abu ne mai ban mamaki kwarai da gaske.

"Yayin da suke yin biris da manyan laifuffukan da wannan kungiyar ta 'yan ta'adda' yan aware ta aikata, wadanda Amurka ta hada kai da su, ta ba da horo da makamai a Siriya, suka yi garkuwa da yara ba kawai a Siriya ba, har ma a yankuna da dama na Iraki, ciki har da Mahmur da Sinjar.

An kuma jaddada cewa, Turkiyya za ta ci gaba da kokarinta, kamar yadda ta saba a baya, don hana aikata laifin safarar mutane.
 


News Source:   ()