Turkiyya ta mayar da 'yan ta'adda 338 zuwa kasashensu

Turkiyya ta mayar da 'yan ta'adda 338 zuwa kasashensu

Kasar Turkiyya ta bayyana cewa ta mayar da 'yan ta'adda data kama a kasarta zuwa kasashensu har guda 338.

Bayanan da suka fito daga ma'aikatar cikin gidan kasar sun nuna cewa ana mayar da 'yan ta'addar da aka kama a cikin kasar Turkiyya zuwa kasashensu.

A bisa haka an mayar da 'yan ta'adda 'yan kasar Beljiyom guda 9.

Akan haka daga ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 2019 kawo yanzu an mayar da 'yan ta'adda zuwa kasashensu a Nahiyar Turai har su guda 113 da kuma wadanda suka hada da 'yan kasar Amurka da Australia. A jumlace an mayar da 'yan ta'adda 338 zuwa kasashensu daga Turkiyya.

 


News Source:   www.trt.net.tr