Turkiyya ta kyamaci hukuncin kotun Turai akan hana daura dankwali

Turkiyya ta kyamaci hukuncin kotun Turai akan hana daura dankwali

Turkiyya ta mayar da martani game da hukuncin da Kotun Tarayyar Turai ta yanke game da hana daura dankwali.

A cikin wata rubutacciyar sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen ta fitar, an bayyana cewa hukuncin da kotun ta yanke kan hana daura dankwali da aka bai wa ma’aikatan wasu kamfanoni biyu daban-daban a Jamus ya keta ‘yancin addini.

"Hukuncin ya zama wani sabon misali na kokarin bayyana kyamar Islama da nuna kyama ga Musulmai a matsayin wadansu lamurra da suka yi katutu a Turai. Hakan wata hanya ce kuma dake nuna wariyar launin fata.
Sanarwar ta kara da cewa,
"A lokacin da kyamar Islama, wariyar launin fata da gubar ƙiyayya da suka yi katutu a Turai, hukuncin kotu akan hana daura dankwali lamari ne dake take hakkin addini a hukumance.
Muna yin Allah wadai da dukkan matakan dake nuna kyama ga addinin Islama da kuma nuna wariyar launin fata."

Kotun Tarayyar Turai ta yanke hukuncin cewa kamfanoni a Tarayyar Turai na iya haramtawa ma’aikatansu sanya hijabi da dankwali karkashin wasu sharudda.


News Source:   ()