Kasar Turkiyya ta yi tir da Allah wadai akan harin ta'addancin da aka kai a kasar Somaliya.
Wata sanarwar da aka fitar ta bayyana cewa muna tare da yar uwarmu kasar Somaliya tare da kuma dukkan alummanta a yaki da ta'addanci.
Ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ce ta fitar da wata sanarwa a rubuce inda ta bayyana cewa ta na bakin cikin samun labarin harin ta'addancin da aka kai da mota dauke da bama-bamai a a wani gidan abinci dake kusa da filin tashi da saukar jiragen saman Mogadishu wandas ya yi sanadiyar rayukan fiye da mutane 20 da kuma raunana wasu 30.
Sanarwar ta kara da cewa "Muna masu matukar kyamatar wannan harin. Muna masui mika sakon ta'aziyya ga alumman da kasar Somaliya baki daya. Muna masu adduar samaun rahamar Allah ga wadanda suka rigamu gidan gaskiya da kuma samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka raunana.