Turkiyya ta kyamaci harin ta'addancin da aka kai kasar Mali

Turkiyya ta kyamaci harin ta'addancin da aka kai kasar Mali

Kasar Turkiyya ta yi tir da Allah wadai akan harin ta'addancin da aka kai a yankin Mopti dake kasar Mali.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya ce ta fitar da sanarwa a rubuce inda take bayyana bakin cikin samun labarin harin ta'addanci da aka kaiwa kawarta Mali.

Sanarwar ta mika ta'aziyya ga hukumar Mali da al'umman kasar akan wadanda suka rasa rayukansu da kuma fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka raunana.

Sanarwar ta kara da cewa "Mun yi bakin cikin samun labarin harin ta'addancin da aka kaiwa barikin sojojin dake Boni wanda ke yankin Mopti a kasar Mali lamarin da ya yi sanadiyar rayukan sojoji da raunanan wasu da dama"

 


News Source:   ()