Turkiyya ta kyamaci harin ta'addancin da aka kai Burkina Faso

Turkiyya ta kyamaci harin ta'addancin da aka kai Burkina Faso

Kasar Turkiyya ta yi Allah wadai da harin ta'addamcin da aka kai kasar Burkina Faso da ya yi sanadiyar rayukan mutum 100.

Kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta sanar, muna bakin cikin samun labarin harin ta'addancin da aka kai yankin Yagha dake kasar Burkina Faso da ya yi sanadiyar rayuka 100.

Muna masu yin tir da Allah wadai akan wannan harin na ta'addanci.

"Muna masu mika sakon ta'aziyya ga 'yan uwan wadanda suka rasa rayukansu da kuma kasar baki daya, muna masu addu'ar samun rahamar Allah ga wadanda suka rasa rayukansu"

 


News Source:   ()