Turkiyya ta bayyana matukar kyama da yin Allah wadai akan harin ta'addancin da aka kai da mota dankare da bama-bamai a gaban wata makaranta dake Kabul babban birnin kasar Afghanistan.
Kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta sanar a rubuce, cikin alhini da bakin ciki mun samu labarin harin ta'addanci da aka kai lokacin bude baki a gaban wata makaranta da mota dauke da bama-bamai a yankin Dasti Archi dake karkashin Kabul babban birnin Afghanistan; lamarin da ya yi sanadiyar rasa rayuka 30 da kuma raunana akallan 50.
Sanarwar ta kara da cewa,
"Muna masu matukar nuna kyama da yin Allah wadai ga irin wannan bakin aikin da aka kai a daren Lailatul Qadir, muna masu yin tir da wadanda suka kai harin, muna kuma fatan dubunsu za ta cika"
Bugu da kari, muna addu'ar samaun rahamar Allah ga wadanda suka rasa rayukansu da kuma samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka raunana.