Turkiyya ta kyamaci harin ta'addanci da aka kai Najeriya

Turkiyya ta kyamaci harin ta'addanci da aka kai Najeriya

Kasar Turkiyya ta yi tir da Allah wadai da harin da kungiyar ta'addar Boko Haram ta kai a garin Pemi dake jihar Borno a kasar Najeriya.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya ce ta fitar da sanarwar a rubuce inda ta bayyana cewa mun yi bakin cikin samun labarin harin da kungiyar ta'addar Boko Haram ta kai garin Pemi lamarin da ya yi sanadiyar rasa rayukan akalan mutane 7.

Sanarwar ta kara da cewa,

"Wannan mummunar harin ta'addancin muna masu kyamatarsa, muna masu addu'ar samun rahamar Allah ga wadanda suka rasa rayukansu, muna kuma mika sakon ta'aziyya ga 'yan uwan wadanda suka rasa rayukansu da kuma ga gwamnatin Najeria da ma ga al'umman kasar baki daya. Muna kuma fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka raunana"

 


News Source:   ()