Kasar Turkiyya ta kyamaci harin da aka kaiwa rundunar 'yan sandan kasar Mali.
Kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya ta sanar a rubuce, mun yi bakin cikin samun labarin harin da aka aki a yankin Bandiagara a kasar Mali lamarin da ya yi sanadiyar rasa rayuka da raunanan wasu da dama.
Sanarwar ta kara da cewa, Muna masu matukar kyamar wannan harin ta'addancin. Muna masu mika sakon ta'aziyya ga kasar Mali da kuma ga al'umman kasar baki daya, muna masu fatan samun rahamar Allah ga wadanda suka rigamu gidan gaskiya da kuma samun sauki cikin gaggwa ga wadanda suka raunana.
Kamar yadda rundunar sojin Mali ta sanar a yankin Bandaigara dake karkashin gundumar Mopti wasu da ba a san ko su wanene ba sun kai harin da ya yi sanadiyar rayukan sojoji 8 da raunanan wasu 5.