Ķasar Turkiyya ta yi tir da Allah wadai akan hare-haren ta'addanci da aka rinka kaiwa jihar Jabo Delgado dake arewacin kasar Mozambique tun daga ranar 24 ga watan Maris kawo yanzu.
Ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ce ta fitar da wata sanarwa a rubuce inda ta yi addu'oin samun rahamar Allah ga wadanda suka rasa rayukansu da kuma fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka raunana.
Sanarawar ta kara da cewa,
"Muna masu ta ya yar uwarmu Mozambique bakin cikin lamarin da ya faru, muna kuma fatan samun zaman lafiya a kasar cikin kankanen lokaci "
Mozambique ta kasance ta na samun gudunmowa daga sojojin hayar Rasha da na Afirka ta Kudu akan domin kalubalantar kungiyar ta'addar Ansar Sunnah da ta bayyana a yankin dake da albarkatun iskar gas shekaru hudu da suka gabata.
Yankin Jabo Delgado mai albarkatun iskar gas da ake yawan kai harin ya kasance akan iyakar kasar da Tanzania.
Sakamakon hare haren da ake kaiwa yankin kawo yanzu mutum fiye da dubu 2 sun rasa rayukansu inda wasu miliyan 1.3 suka kasance cikin matsalar tsaro.
Haka kuma sakamakon harin ta'addancin da kungiyar ta'addar Ansarul Sunna ke kaiwa a Mozambique mutum dubu 670 sun rasa matsugunansu.
Wadanda suke kai harin da alumman yankin ke kira da sunan Ashabab an bayyana cewa suna da alaka da kungiyar ta'addar Deash.