Turkiyya ta kara daura damarar bunkasa tattalin arziki

Turkiyya ta kara daura damarar bunkasa tattalin arziki

Ministan tattalin arziki da baitul malin kasar Turkiyya Berat Albayrak a taron Kwamitin Daidaito da Bunkasa Tattalin Arziki (FİKKO) ya bayyana cewar sun duba da tuntubar hukumomin tattalin arzikin kasa da kasa a shirin bunkasa tatalin arzikin kasar.

Berat Albayrak, ya yada a shafinsa ta Twitter da cewa FIKKO ta gudanar da taronta na watan Agusta inda ya kara da cewa,

"A shirin bunkasa tattalin arzikin kasa, an dubu halin da tattalin arzikin kasa da kasa yake ciki. Da yardan Allah zamu ci gaba da samun bunkasar da muka samu a cikin shekarar 2020 a shekara mai zuwa"

 


News Source:   ()