Turkiyya ta kalubalanci harin da Armeniya ta kaiwa Azerbaijan

Turkiyya ta kalubalanci hare-haren da Armeniya ta fara kaiwa sansanonin sojin Azerbaijan da kuma yankunan farar hula a wasu bangarorin kasar Azerbaijan.

Shugaban zauren majalisar kasar Turkiyya  (TBMM) Mustafa Şentop, ya yada a shafin sadar da zumunta ta twitter da cewa, Turkiyya za ta cigaba da kasancewa tare da kasar Azerbaijan da dukkan karfinta.

Şentop ya kara da cewa,

"Armeniya ba ta kasance mai kalubalantar kasar Azerbaijan kawai ba, ta kuma kasance kasar ta'addanci dake kalubalantar zaman lafiyar yankin baki daya, a sabili da haka zata dauki alhakin dukkanin matsalolin da hakan zai haifar. Turkiyya za ta ci gaba da kasancewa tare da Azerbaijan da dukkanin karfinta"

Haka kuma, mai magana da yawun shugaban kasar Turkiyya Ibrahim Kalın a shafinsa ta Twitter ya bayyana cewa kaiwa farar hula hari da Armeniya ta yi ya sabawa yarjejeniyar tsagaita wuta.

Ya kara da cewa "Ya zama wajibi ga hukumomin kasa da kasa su yi kira da dakatar da irin wannan danyen aikin. Turkiyya dai za ta cigaba da kasancewa tare da Azerbaijan. Muna masu addu'ar Allah ya ji kan wadanda suka rasa rayukansu a harin. Azerbaijan ba ta kasance ita daya ba domin Turkiyya na tare da ita."

Mai magana da yawun Jam'iyyar Adalci da Ci gaba mai mulkin kasar Turkiyya watau AK Party Ömer Çelik, a Twitter inda ya bayyana cewa muna masu matukar kyamatar harin da Armeniya ta kaiwa Azerbaijan ya kuma kara da cewa,

"Armeniya ta kara nuna irin halinta na karya doka da tsokana. Wannan aika-aikan na Armeniya laifin ne akan bil adama. Domin kalubalantar Armeniya ya kamata hukumomin kasa da kasa su tsawata mata"

 


News Source:   ()