Turkiyya ta kalubalanci Austriya akan zargin Erdogan

Turkiyya ta kalubalanci Austriya akan zargin Erdogan

Turkiyya ta sanar da cewa zarge-zargen da Ministan Hadakar kasar Austriya Susanne Raab ke yi game da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ba gaskiya ba ne kuma ba za a amince da su ba.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya, Ambasada Tanju Bilgic, a cikin rubutaccen martanin da ya mayar game da batun ya bayyana cewa,

"Ministan Hadin kan Austriya Susanne Raab, a wani taron manema labarai da aka gudanar jiya (ranar da ta gabata), ta bayyana cewa amincewa da taswirar da 'Cibiyar Tattara bayanan Musulunci ta Siyasa' wanda kungiyoyin Musulmai a Austria suka tsara, da jawaban da shugaban kasarmu ya yi ya tayar da kayan baya a kasar- wannan ba gaskiya ba ne kuma ba abinda za'a amince dashi ba ne"

Bilgic ya bayyana cewa wadannan manufofin kyamar baki, wariyar launin fata da kuma kyamar Islama suna cutar da hadin kan jama'a.

"Yana da muhimmanci ga Ostiriya da ta yi watsi da wannan yunkurin, wanda ya shafi baki da Musulmai, kuma ta dauki hanyar gudanar da siyasa mai kyau"


News Source:   ()