Turkiyya ta kaddamar da Farmakin "Eren-10 Gabar" domin yaki da ta'addanci

Turkiyya ta kaddamar da Farmakin "Eren-10 Gabar" domin yaki da ta'addanci

Ma'aikatar cikin gidan kasar Turkiyya ta sanar da kaddamar da Farmakin "Eren-10 Gabar" a yankin Sirnak-Siirt domin ci gaba da yaki da kungiyar ta'addar PKK.

Kamar yadda ma'aikatar ta sanar, an kaddamar da wannan farmakin ne da zummar magance dukkanin mambobin kungiyar ta'adda dake yankin.

A farmakin dakaru 1073 ne ke halarta.

A faramkin Eren da aka kaddamar a ranar 11 ga watan Janair 2021 kawo yanzu an magance 'yan ta'adda 3. Haka kuma an kame masu aiki tare da 'yan ta'dda harsu 58 tare da lalata mabuyar 'yan ta'addan 213 da kuma guraren boye makamansu.

 


News Source:   ()