Turkiyya ta fitar da sakon ta'aziyya akan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon fashewar tankin mai a Lebanon.
A cikin rubutacciyar sanarwa daga Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar Turkiyya,
"Mun samu labari cikin bakin ciki, bisa rahotannin farko dake nuna cewa mutane 22 sun rasa rayukansu kuma da yawa sun jikkata sakamakon fashewar tankar man fetur a yankin Akkar na arewacin Lebanon."
A cikin sanarwar an kara da cewa,
"Muna fatan samun rahamar Allah ga wadanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan lamari, muna jajantawa 'yan Lebanon da 'yan uwan wadanda suka rasa rayukansu, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa."