Turkiyya ta ja kunnen Girka akan kashe wani dan kasar Turkiyya

Turkiyya ta ja kunnen Girka akan kashe wani dan kasar Turkiyya

An ja kunnen Girka akan kashe dan kasar Turkiyya sanadiyar bude wuta daga bangaren Girka a yankin Edirne.

Wani dan kasar Turkiya ya mutu a Edirne, da misalin karfe 19.20 na jiya, sakamakon harbin da wani mutum ko mutanen Girka suka yi masa.

Dangane da bayanan da aka samu daga majiyoyin Ma’aikatar Harkokin Waje, an gayyaci mai kula da ofishin jakadancin Girka da ke Ankara zuwa ma’aikatar dangane da lamarin kuma an ba da takardar da ke dauke da martani akan lamarin.

An ba da rahoton cewa mai kula da ofishin jakadancin ya bukaci a binciki wannan lamarin kuma a sanar da dashi sakamakon, a kama wanda ya yi kisan kuma a hukuntashi, sannan a dauki matakan hana sake aukuwar hakan.

Bugu da kari, an bayyana cewa hakkokin wadanda aka kashe da danginsu na diyya an tanade su.


News Source:   ()