Turkiyya ta gudanar da atasaye a iyakokin ruwan Libiya

Turkiyya ta gudanar da atasaye a iyakokin ruwan Libiya

Ma’aikatar tsaron kasar Turkiyya ta sanar da cewa rundunar sojinta ta sama ta gudanar da wasu atasaye a iyakokin Libiya.

Ma’aikatar ta kara da cewa an gudanar da atasayen ta amfani jiragen kirar TCG da kuma jirage masu saukar ungulu a cikin jiragen ruwa a yankin ruwan Libiya.

Halastacciyar gwamnatin Libiya dai da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa a shekarar 2015 bayan kauda mülkin Muammar Gaddafi a 2011 na ci gaba da fuskantar kalubaloli da suka kunshi hare-hare daga mayakan Haftar.

An ‘yan kwanakin dai gwamnatin kasar ta dauki manyan matakan kalubalantar mayakan na Haftar.

Turkiyya ta kasance tana goyon bayan halastacciyar gwamnatin kasar da MDD ta kafa da kuma kira da abi hanyar diflomasiyya domin kawo karshen rikicin kasar.


News Source:   ()