Shugaban kasar Yukiren Vladimir Zelenskiy ya sanar da cewa, an fara kera sabon jirgin ruwan yakin kasarsa a Turkiyya.
Zelensky, a cikin jawabinsa a bikin da aka yi a Odessa domin Ranar Sojojin Ruwan Ukraine ya kara da cewa,
“Abokanmu a Turkiyya sun mayar da himma don ci gaban da samar da jirgin ruwan Yukiren. An fara aikin samar da jirgin a Turkiyya kuma za'a kammala shi a Yukiren a karshen shekarar 2023.
Zelenskiy ya bayyana cewa, Yukiren na sa ran karbar jiragen sama marasa matuka na Bayraktar daga Turkiyya nan ba da jimawa ba. Inda ya kuma kara da cewa,
“Ana ci gaba da ayyukan samar da jirgin mu na ruwa. Muna sa ran karban jirage marasa matuka na Bayraktar a nan gaba kadan. ”
An sanya hannu kan yarjejeniyoyi tsakanin Turkiya da Yukiren a fagen rukunin dakaru na ADA akan jirage marasa matuka domin biyan bukatun sojojin ruwan kasar Yukiren.