Turkiyya ta daura damarar goyon bayan Falasdin a matakin kasa da kasa

Turkiyya ta daura damarar goyon bayan Falasdin a matakin kasa da kasa

Turkiyya ta daura damarar goyon bayan Falasdin a matakin kasa da kasa da a duniyar Musulmi kamar yadda wani jami’ain maikatan turkiyya ya bayyana yayinda yake kalubalantar irin rikon sakainar kashin da duniya ke yiwa maslahar Falasdinu.

Shugaban Hukumar Turkawa da Kawaye ta YTB Abdullah Eren ya tattauna akan ranar Nakba, Ranar Cin Zarafi, da kuma hare-haren da Isra’ila ta kaiwa Falasdinawa kwanakin nan.

Ranar Nakba dair ana ce da aka tilastawa Falasdinawa dubu 800 ficewa daga gidajensu a shekarar 1948.

Eren ya bayyana cewa duk da duniya na ko oho da matsalar Falasdinawa, Turkiyya za ta cigaba da goyon bayan ‘yancin kasar a matakin kasa da kasa.


News Source:   ()