Turkiyya ta sanar da dakatar da safarar jiragen sama na wucin gadi daga kasashen duniya 4 da suka hada da; Ingila, Denmark, Holan da Afirka ta Kudu.
Ministan Lafiya na Turkiyya ya shaida cewa, "An samu karin yaduwar cutar Corona sosai a kasar Ingila. Sakamakon umarnin da Shugaban Kasarmu Recep Tayyip Erdogan ya bayar, tare da hadin kan Ma'aikatar Sufuri da Gina Kasa, an dakatar da zuwan jiragen sama Turkiyya na wucin gadi daga kasashen Ingila, Denmark, Holan da Afirka ta Kudu."
Ya kuma ce "A karkashin matakin da aka dauka, za a yi gwajin cutar tare da killace mutanen da ke cikin jiragen saman da suka riga suka taso daga kasashen zuwa Turkiyya."
Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewar, cutar Corona ta saura salo da yanayi a kasashen Ingila, Holan, Denmark da Ostireliya.