Turkiyya ta ce ta yi maraba da tsagaita bude wuta da gwamnatin Habasha ta ayyana a Tigray a ranar 28 ga watan Yuni.
A cikin wata rubutacciyar sanarwa daga Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya an bayyana cewa,
"Muna la'akari da tsagaita wutar da aka sanar don kawo karshen tashin hankali a yankin da wuri-wuri kuma don tabbatar da cewa an kai kayan agaji ga yankin ba tare da wata tsangwama ba, mataki ne da ya dace don magance rikicin da ke faruwa yanzu."
A cikin sanarwar, an jaddada cewa Turkiyya za ta ci gaba da tallafawa kokarin kiyaye zaman lafiya, da samar da kwanciyar hankali a Habasha, wacce take da alakar tarihi da ita.
Gwamnatin Habasha ta sanar a ranar 28 ga Yuni cewa, ta ayyana tsagaita bude wuta a wani yanki a yankin Tigray, wanda ake zargin ‘yan tawayen TPLF sun kame.
A cikin sanarwar, an lura cewa an dauki wannan shawarar ne domin baiwa manoman jihar damar yin amfani da lokacin girbinsu a watannin (Yuni, Yuli, Agusta), kuma an bayyana cewa daga yanzu, kungiyoyin agaji a yankin zasu yi aiki ba tare da tallafin sojoji ba.
A cikin sanarwar, an bayyana cewa har yanzu sojojin na TPLF suna cikin wata tarwatsa a yankin kuma suna kai hare-hare lokaci zuwa lokaci.