Turkiyya ta aike da sakon ta'aziyya ga kasar Indonesiya

Kasar Turkiyya ta aike da sakon ta'aziyya ga kasar Indonesiya akan annobar ambaliyar ruwa da ta afku a jihar Nusa Tenggara dake gabashin kasar.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya ce ta yada sakon cewa, mun yi bakin cikin samon labarin afkuwar annobar ambaliyar ruwa a jihar Nusa Tenggara dake gabashin Indonesiya.

Sanarwar ta kara da cewa,

"Muna addu'ar samun rahamar ubangiji ga wadanda suka rasa rayukansu, muna kuma fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka raunana, muna kuma masu mika sakon ta'aziyya ga 'yar uwarmu kasar Indonisiya"

Mai magana da yawun Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasar Indonesiya Raditya Jati ne ya sanar da cewa a garin Flores dake jihar  Nusa Tenggara an samu afkuwar ambaliyar ruwan da ta yi sanadiyar rayuka mutane 44 da kuma raunanan wasu mutum 9.

 


News Source:   ()