Turkiyya ta aike da sakon jaje da ta'aziyya ga China

Turkiyya ta aike da sakon jaje da ta'aziyya ga China

Turkiyya ta aike da sakon jaje da ta'aziyya ga China sakamakon ibtila'İn ambaliyar ruwa da ya afku a jihar Henan.

Rubutacciyar sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar ta ce, sun yi bakin ciki da samun labarin mutuwar mutane sama da 25 tare da batan wasu da dama sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a yankin Henan.

Sanarwar ta ce, "Muna mika sakon jaje da ta'aziyya ga makusantan wadanda suka mutu, gwamnati da jama'a China baki daya, muna kuma fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata."

 


News Source:   ()