“Turkiyya shirye take ta tattuana da ko wace kasa akan ko wace irin matsala”

“Turkiyya shirye take ta tattuana da ko wace kasa akan ko wace irin matsala”

Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cagusoglu ya bayyana cewa kofofin Turkiyya bude suke domin tattaunawa da ko wace kasa da take da matsaloli da ita.

A yayinda da yake jawabi a taron Mediterranean Dialogue Forum karo na shida da ma’aikatar harkokin wajen Italiya da Cibiyar Nazarin Siyasar Kasa da Kasa ta shirya, Cavusoglu ya yi sharhi akan huldan Turkiyya da kasashen Nahiyar Turai da kuma Amurka da ma matsalolin da ke fuskantar yankin Gabashin Bahar Rum.

Ya jaddada shirin Turkiyya na zama teburin sulhu domin tattaunawa da kasashe Faransa da Austria domin warware matsalar dake tsakaninsu a halin yanzu, inda kuma ya soki matakan da gwamnatocin Faransa da Austria suka dauka a ‘yan kwanakin nan dake kalubalnatar Musulmi.


News Source:   ()