Turkiyya na neman kawayenta su ba da cikakken goyon bayan yaki da ta'addanci

Turkiyya na neman kawayenta su ba da cikakken goyon bayan yaki da ta'addanci

Kasar Turkiyya ta bayyana tsammanin cewa kawayenta zasu bayar da cikekken goyon baya domin yaki da ta’addanci.

Mai magana da yawun jam’iyyar AK Parti mai mulkin kasar Turkiyya Omer Celik ya yi sharhi akan kalaman Amurka bayan taron da ya halarta a Ankara.

Omar ya bayyana cewa a yayinda muke tsammanin kawayenmu za su mutunta demokradiyyarmu, ba zamu amince da bayanan da zai kalubalanci ma’aikatun shari’armu ba.

"Muna tsamanin a girmama demokradiyyarmu, muna kuma tsammanin a girmama shari’armu”

Jawabin Celik na zuwa ne bayan kashe ‘yan kasar Turkiyya 13 da kungiyar ta’addar PKK ta yi a Arewacin Iraki.


News Source:   ()