Jami'an tsaron kasar Turkiyya sun sake kubutar da 'yan gudun hijira 56 da Girka ta kora zuwa yankin tekun Ayvacik dake yankin Canakkale na Bahar Aswad.
Jami'an tsaron sun samu labarin cewa akwai yan gudun hijira cikin kwalekwalen roba dake neman a kai musu dauki a gabar tekun Kadirga Burnu.
An dai yi nasarar kubutar da 'yan gudun hijiran su 56 da jami'an tsaron Girka suka kora cikin teku.
Bayan an kammala bincike an mika su ga hannun hukumar kula da baki dake yankin.