Ana ci gaba da kokarin kwashe 'yan kasar Turkiyya daga Afganistan.
A cikin wannan yanayin, an kara kwashe mutane 160 daga babban birnin kasar, Kabul, ta jirgin sama na rundunar sojin saman Turkiyya.
Fasinjojin da aka kai su Pakistan ma jirgin saman Turkish Airlines dauko su zuwa Istanbul daga can.
'Yan Taliban da suka kewaye Kabul babban birnin kasar a ranar Lahadin da ta gabata, sun karbe ikon birnin ba tare da rikici ba yayin da shugaba Ashraf Ghani ya bar kasar inda kuma sojojin gwamnati suka bar babban birnin.