Kasar Turkiyya na ci gaba da kubutar da 'yan gudun hijrar da kasar Girka ke ci gaba da korasu zuwa cikin teku. Akan haka an kubutar da wasu masu neman mafakan 28 a yankin tekun Ayvacik a Çanakkale.
Masu neman mafakar sun tunkari tsibirin Midilli dake yankin Girka a cikin kwale-kwalen roba.
Dakarun kasar Turkiyya sun hango masu neman mafakar su 28 da jami'an Girka suka tunkudo zuwa Bahar Aswad dake yankin Turkiyya.
Jami'an tsaron kasar Turkiyya sun kubutar da masu neman mafakar a yankin Sivrice Burnu inda suka kaisu ofishin 'yan sandan dake Küçükkuyu a yankin Ayvacik.